logo

HAUSA

Ba za a taba maye gurbin matsayin MDD ba

2022-10-24 20:16:26 CMG Hausa

 

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba gudanarwa Litinin din nan cewa, a rana mai kaman ta yau shekaru 77 da suka wuce, kundin tsarin mulkin MDD ya fara aiki, aka kuma kafa MDD, matakin da ya bude wani sabon babi na raya huldar dake tsakanin kasashen duniya.

A matsayinta na kungiyar kasa da kasa mafi girma a duniya, wakiliya kuma mai karfin fada a ji a duniya, MDD ta himmantu wajen inganta ra'ayin kasancewar bangarori, kana ta taka rawar da ba za ta iya maye gurbinsa ba wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya, da raya ci gaba cikin hadin gwiwa.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, har kullum kasar Sin tana kiyaye manufofi da ka'idojin kundin da ke cikin tsarin mulkin MDD, da ma babban rawar da MDD ke takawa a harkokin dake shafar kasashen duniya. Kasar Sin ta kuduri aniyar tabbatar da zaman lafiya a duniya baki daya, da ba da gudummawa ga ci gaban duniya, da ma kiyaye tsarin kasa da kasa.(Ibrahim)