logo

HAUSA

Jagororin EU sun amince da bukatar fitar da tsarin shawo kan hauhawar farashin makamashi

2022-10-22 15:40:33 CMG Hausa

Jagororin kungiyar tarayyar Turai ta EU, sun amince da bukatar fitar da wani sabon tsari, mai kunshe da matakan kare al’ummar Turai daga kalubalen hauhawar farashin makamashi.

A jiya Juma’a ne aka cimma matsayar bayan shafe sa’o’i ana tattaunawa, game da shawarwarin sauko da farashin makamashin, wanda ya yi tashin gwauron zabi sakamakon rikicin Rasha da Ukraine.

Bayan kammalar taron, shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen, ta shaidawa taron manema labarai cewa, an amince da kafa wani tsari mai inganci, wanda zai mayar da hankali ga batun farashin makamashi.

Ta ce jagororin kungiyar sun bukaci ministocin makamashi daga kasashe mambobin kungiyar, da su mika tabbatattun kudurori masu nasaba da farashin wucin gadi, wanda za a aiwatar kan farashin iskar gas, wanda zai dakile hauhawar farashin, da ma kayyadadden farashin gas da ake amfani da shi wajen samar da lantarki.

Har ila yau, shugabannin na EU sun amince da bukatar aiwatar da manufofin sayen iskar gas, ta amfani da dandalin bai daya kafin lokacin hunturu dake tafe. (Saminu Alhassan)