logo

HAUSA

Dabbobin Panda na kasar Sin sun isa Qatar

2022-10-20 11:04:29 CMG Hausa

Kasar Qatar ta yi maraba da isar dabbobin Panda biyu kasar, karkashin wani shirin hadin gwiwa na farko, dake tsakaninta da kasar Sin kan bincike da kare dabbar Panda.

Da isarsu Doha, babban birnin Qatar, nan take aka garzaya da dabbobin Pandar da suka hada da mace mai shekaru 3 mai suna Si Hai da namiji mai shekaru 4 mai suna Jing Jing, zuwa gidan Panda dake wurin yawaon shakatawa na Al Khor, inda zai kasance sabon mazauninsu.

Haka kuma, kasar Qatar ta sanya musu sunan harshen Larabci, inda Jing Jing ya samu sunan Suhail, yayin da aka sanyawa Si Hai, Soraya.

Mohammed Al Khouri, daraktan sashen kula da wuraren shakatawa na ma’aikatar kula da biranen Qatar, ya shaidawa Xinhua cewa, bisa al’adar Larabawa, Suhail da Soraya taurari ne dake sararin samaniya, wadanda ke alamta nasara da daukaka da daraja.

Ya kara da cewa, Qatar za ta hada hannu da takwarorinta na Sin, wajen gudanar da bincike kan yanayin dabbobin Panda dake iya rayuwa a hamada.

Yayin bikin marabar da aka yi a wajen shakatawa na Al Khor, Jakadan Sin dake Qatar Zhou Jian, ya ce hadin gwiwa game da bincike da kare dabbobin Panda dake tsakanin Sin da Qatar, ita ce irinta ta farko a yankin Gabas ta Tsakiya, wadda kuma ke nuna sabon matsayin dangantar Sin da Qatar. (Faeza Mustapha)