logo

HAUSA

Sin ta yi kira da a karfafa nasarorin zaman lafiya da aka samu a CAR

2022-10-20 11:01:04 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira da a yi kokarin karfafa nasarorin da aka samu na wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, wato CAR a takaice.

A cewar Geng Shuang, yanayin siyasa da na tsaro a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na ingantuwa, kuma ana samun ci gaba a bangaren wanzar da zaman lafiya. Sai dai, har yanzu da sauran matsaloli da kalubale, yana mai cewa, ya kamata kasashen duniya su kara tallafawa wajen inganta zaman lafiya da ci gaba.

Ya kara da cewa, gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, tana aiwatar da sakamakon tattaunawar kasa da aka yi, wanda ke nuna kyakkyawan sakamakon da aka samu daga tattaunawa da kungiyoyin masu dauke da makamai da inganta kwance damarar makamai, domin bunkasa aikin wanzar da zaman lafiya.

Biyo bayan baza jami’an gwamnati a fadin kasar, yanayin tsaro na ingantuwa a shekarun baya-bayan nan, kuma ayyukan kungiyoyi masu dauke da makamai na raguwa. A cewar Geng Shuang, takunkuman kwamitin sulhu na mummunan tasiri ga karfin kasar na tabbatar da tsaro, don haka akwai bukatar a dage su. 

Ya ce kasar na fuskantar matsalolin kudi da makamashi da karancin abinci da matsalolin tattalin arziki da na zamantakewa masu tsanani, inda kaso 60 na al’umma ke bukatar agajin jin kai. Ya ce ya kamata kasa da kasa da hukumomi su dawo da bayar da tallafi ba tare da bata lokaci ba, domin taimakawa kasar magance matsalolinta na tattalin arziki da jin kai.  (Fa’iza Mustapha)