logo

HAUSA

Tsarin dimokuradiyya na kasar Sin ya nuna basirar Sinawa

2022-10-20 10:56:34 CMG Hausa

 

Yanzu haka ana gudanar da taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a birnin Beijing na kasar, inda a cikin rahoton da Xi Jinping, babban sakataren jam’iyyar, ya gabatar a wajen taron, ya nanata tsarin dimokuradiyya na musamman na kasar, wanda ya shafi dukkan fannonin ayyukan gwamnatin kasar.

Wannan tsarin ya ba jama’ar kasar Sin damar yin zabe, da tattaunawa da tsai da kuduri game da manufar da za a gabatar, da kulawa da sa ido kan harkokin gwamnati, duk bisa akidar dimokuradiyya. Maimakon a jefa kuri’a kawai, sa’an nan a dakatar da aiwatar da ikon dimokuradiyya.

Tsarin dimokuradiyyar Sin ya jibanci dukkanin al’ummar kasar, inda suke iya halartar ayyukan siyasa kai tsaye, ba tare da kasancewa karkashin wata jam’iyyar siyasa ba. A ganin Sinawa, don aiwatar da tsarin dimokuradiyya da kyau, ya kamata a sanya al’ummun kasar su shiga a dama da su, a fannin gudanar da harkokin mulki a kasar.

Wata karin maganar kasar Sin ita ce, “Mai takalma shi kadai ya san ko takalmansa sun dace da kafafuwansa”. Ya kamata a ba jama’ar wata kasa damar tabbatar da salon tsarin dimokuradiyyarsu. Idan aka tilasta wata kasa daukar tsari irin na sauran kasashe, to, wannan manufar ce ta nuna fin karfi, ba dimokuradiya ba. (Bello Wang)