logo

HAUSA

Sin: A ci gaba da daidaita yanayi a kasar Mali

2022-10-19 10:58:51 CMG Hausa

Dai Bing, mukaddashin jakadan kasar Sin a MDD, ya gabatar da jawabi a yayin taron kwamitin sulhun majalissar game da Mali, da ya gudana jiya Talata, inda ya yi kira da a ci gaba da kokarin daidaita yanayin da ake ciki a kasar Mali, musamman ma a fannin harkokin siyasa.

Mista Dai ya ce, zuwa yanzu an samu ci gaba a fannin shirin mika mulki, da yaki da ayyukan ta’addanci a kasar Mali. Don haka, ya kamata a kiyaye wannan yanayi mai kyau da ake ciki, da kara kokarin wanzar da dauwamamen zaman lafiya da ci gaba a kasar.

Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin na dora muhimmanci kan bukatun kasar Mali a fannonin ikon mulkin kai, da tsaro, da raya kasa, kana tana goyon bayan al’ummar kasar da su zabi hanyar raya kasa da ta dace da yanayin kasarsu.

Jami’in na Sin ya bayyana cewa, kasar Sin na son samar da karin taimako ga kasar Mali, a kokarinta na tabbatar da hadin kan kasa, da samun zaman lafiya da ci gaba. (Bello Wang)