logo

HAUSA

Yadda za a samu ci gaba mai inganci a wurare daban daban na kasar Sin ke jan hankali

2022-10-19 14:41:20 CMG HAUSA

 

Rahoton da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin bikin bude babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, ya bayyana cewa, samun bunkasuwa mai inganci shi ne aikin farko na gina kasa mai karfi kuma mai bin tsarin gurguzu ta zamani daga dukkan fannoni.

A yayin taron manema labaru da aka gudanar a cibiyar yada labaru na babban taron jiya Talata, a karon farko an gayyaci kakakin kungiyoyin wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na larduna da na jihohi masu zaman kansu da na manyan biranen wadanda suke karkashin shugabancin gwamnatin tsakiya kai tsaye guda 7, ciki har da na Beijing da Shanxi da Liaoning, da su bayyana yadda wakilan jam’iyyar su suke nazari da kuma tattaunawa kan rahoton. A cikin bayanansu, mai taken “Ci gaba mai inganci” ya zama muhimmiyar kalmar da su kan ambata.

Mai magana da yawun tawagar birnin Beijing, zaunannen mamba, kana babban sakataren kwamitin JKS na reshen birnin Beijing Mr. Zhao Lei ya bayyana cewa, Beijing shi ne birni na farko a cikin manyan birane na kasar da ya rage yawan abubuwan da ko da yake suna amfanawa ci gaban birnin, amma ba su da inganci kamar yadda ake fata. Don haka dole ne a dage wajen rage yawan shigar da abubuwan da ba za a iya sabuntawa ba, a waje daya kuma, dole ne a kara yawan shigar da sabbin abubuwan da aka kirkiro.

Sannan mai magana da yawun tawagar lardin Shanxi, kuma zaunannen mamban kwamitin jam'iyyar kwaminis reshen lardin Shanxi, kana mataimakin gwamnan dindindin na lardin, Mr. Zhang Jifu ya ce, lardin Shanxi na daukar matakan sauya salon raya masana'antu, da raya masana’antun fasahohin zamani a lokaci guda, a kokarin neman ci gaba mai inganci.

Kakakin tawagar Liaoning, kuma mataimakin sakataren kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin reshen lardin Liaoning Mr. Hu Yuting, ya bayyana cewa, an dauki managartan matakan neman farfadowar Liaoning a sabon zamani, sakamakon haka, lardin Liaoning zai taka rawar a zo a gani wajen farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin gaba daya a sabon zamani. (Safiyah Ma)