logo

HAUSA

Kasar Sin na kokarin taimakawa kasashe daban daban samun isashen abinci

2022-10-19 15:44:34 CMG Hausa

Cikin rahoton da babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), Xi Jinping ya gabatar a yayin bude taron wakilan jam’iyyar karo na 20, a ranar Lahadi da ta gabata, Mista Xi ya sake jaddada bukatar samar da isashen abinci, da kare fadin gonaki don tabbatar da ganin fadinsu bai yi kasa da kadada miliyan 120 ba, ta yadda kasar za ta iya dogaro da kanta wajen samun isashen abincin da take bukata.

Yanzu haka kasar Sin tana amfani da gonakin da fadinsu bai kai kaso 9 na fadin gonakin duniya ba, wajen samar da hatsin da yawansa ya kai rubu’in daukacin hatsin da ake samarwa a duniya. Wannan na zuwa ne, yayin da gwamnatin kasar Sin ke kokarin zamanintar da aikin gona, da karfafa aikin samar da hatsi a kai a kai.

Ban da wannan kuma, kasar Sin ta sha samar da tallafi na abinci ga kasashen da ke da bukata, don karfafa akidar jin kai, da taimakawa daidaita matsalar karancin abinci a duniya.

Cikin rahoton nasa, Mista Xi Jinping ya bayyana niyyarsa ta hadin gwiwa tare da sauran kasashe wajen aiwatar da shawarwarin da kasar Sin ta gabatar, na tabbatar da ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya a duniya. Hakan, ya nuna cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kokarin samar da gudunmawa ga aikin tabbatar da samar da isashen abinci a sassan duniya, da kafa al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama. (Bello Wang)