logo

HAUSA

Harbe-harben da suka faru a wasu sassan Amurka sun haddasa mutuwar mutane 4 kana wasu 30 sun jikkata

2022-10-17 13:53:57 CMG HAUSA

 

Jaridar Capitol Hill da ake bugawa a kasar Amurka, ta bayar da rahoto cewa, tun daga Asabar zuwa jiya, harbe-harbe da dama sun faru a wasu jihohin Amurka, wadadnda suka haddasa mutuwar mutane 4 yayin da mutane a kalla 30 suka jikkata.

Rahotanni na cewa, harbe-harben da aka yi a jihohin Virginia and Georgia sun faru ne a jiya Lahadi, inda wani dan bindiga ya bude wuta kan jama’a yayin da ake wani gangami, lamarin da ya jikkata mutane 8.

Kana harbe-harben da aka yi a jihohin Colorado, Massachusetts, da New York da Pennsylvania kuwa, duk sun faru ne a ranar Asabar, inda aka kashe mutane 4.

Bayanai na nuna cewa, ana yawaitar samun harbe-harben bindiga a sassan Amurka, alkaluman kididdigar da shafin intanet dake bayani kan matsalar harbe-harben bindiga a Amurka mai suna “gun violence archive”, ya bayyana cewa a shekarar bana harbe-harbe masu tsanani fiye da 500 ne suka faru a cikin Amurka. (Safiyah Ma)