logo

HAUSA

Xi Jinping: JKS za ta yi aiki tukuru wajen dinke sassan kasa

2022-10-16 13:04:29 CMG Hausa

Cikin rahoton da ya gabatar a yayin bikin bude babban taron wakilan JKS na 20, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce JKS za ta aiwatar da dukkanin manuofi da za su ba da damar warware batun yankin Taiwan a sabon zamani, tare da tabbatar da cimma burin dinkewar sassan kasa.

Shugaba Xi ya ce warware batun Taiwan harka ce ta kasar Sin, wadda ya zama wajibi Sin din ta magance ta. Ya ce "Za mu ci gaba da yin aiki tukuru, domin warware wannan batu cikin lumana bisa gaskiya da kwazon aiki, amma ba za mu alkawarta kore yiwuwar amfani da karfi ba, kana muna da nufin duba yiwuwar daukar dukkanin matakai. Ya kamata masu kokarin tsoma baki na waje, da kuma masu burin ballewar yankin Taiwan da dukkanin ayyukansu su san haka. Ban ambaci hakan domin ’yan uwan mu na Taiwan ba”.  (Saminu Alhassan)