logo

HAUSA

Mataimakin Shugaban Kasar Sin Ya Gana da Shugaban Kazakhstan Da Halartar Taron CICA

2022-10-14 12:19:09 CMG Hausa

Ranar 13 ga wata, shugaban kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev, ya gana da mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan a birnin Astana, babban birnin kasar.

A yayin ganawar, Tokayev ya bukaci Wang Qishan da ya isar da sakon gaisuwa da fatan alheri ga shugaba Xi Jinping na kasar Sin. Shugaban ya yaba wa muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a fannin taimakawa juna, da amincewar juna a tsakanin kasashen Asiya. Ya nuna cewa, babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20 da za a bude a karshen wannan mako, wani kasaitaccen taro ne da ke da ma’ana a tarihi, zai kuma bude sabon shafi na zamanintar da kasar Sin ta gurguzu daga dukkan fannoni, da kaddamar da aikin kafa kasar Sin mai tsarin gurguzu ta zamani mai wadata, da bin tsarin demokuradiyya, da wayin kai da jituwa nan da shekarar 2049, wato yayin da za a cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin.

A ranar 13 ga wata kuma, Wang Qishan ya halarci taron koli karo na 6, na taron taimakawa juna, da daukar matakan amincewa da juna na Asiya wato CICA a takaice, inda a cikin jawabinsa, ya ce, ya kamata a inganta hadin kai da taimakawa juna, a daidaita kalubale yadda ya kamata, a kokarin raya makomar bai daya ta Asiya mai kyau. Wang ya jaddada cewa, har kullum kasar Sin na ji dadin ganin bunkasar CICA daga hangen nesa, da manyan tsare-tsare. Kuma za ta taka rawa a sassa masu ruwa da tsaki, kana za ta gudanar da harkokin mu’amala a fannonin aikin gona, da raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, da hada-hadar kudi, da bunkasa cibiyoyin kwararru da dai sauransu.

Ya ce Sin tana son hada kai da bangarori masu ruwa da tsaki, wajen daga CICA zuwa sabon mataki. (Tasallah Yuan)