logo

HAUSA

WHO da UNICEF sun bukaci a zuba karin jari a fannin kula da lafiyar kwakwalwa a Afirka

2022-10-11 11:11:31 CMG Hausa

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, da asusun kananan yara na majalissar ko UNICEF, sun bukaci a zuba karin jari a fannin kiwon lafiyar kwakwalwa a nahiyar Afirka, duba da yadda barkewar annobar COVID-19 ya haifar da karin gibi, game da samun kulawar lafiyar kwakwalwa tsakanin al’ummun nahiyar.

WHO da UNICEF sun fitar da sanarwar hadin gwiwa a birnin Nairobin kasar Kenya a jiya Litinin, albarkacin ranar kiwon lafiyar kwakwalwa ta duniya, inda suka jaddada burinsu na shiga a dama da su, wajen daga martabar kiwon lafiyar kwakwalwa.

Da yake tsokaci game da hakan, daraktan shiyyar gabashi da kudancin nahiyar Afirka a asusun UNICEF Mohamed M. Fall, ya ce tasirin tashe tashen hankula da matsalolin jin kai, sun wuce batun tattalin arziki kadai, domin kuwa suna haifar da wani ciwo da ba a iya gani a zahiri, wanda ya kamata a mayar da hankali ga magance shi.

Hukumomin MDDr biyu sun ce an shafe watanni 12 da suka gabata cikin matsi, sakamakon kalubalen sauyin yanayi, da hauhawar farashin kayayyaki da matsin tattalin arziki.

Sun kuma ce nahiyar Afirka na fuskantar babban gibin kiwon lafiyar kwakwalwa, saboda rashin zuba isasshen jarin kandagarki, da shawo kan matsalolin wannan bangare na kiwon lafiya.  (Saminu Alhassan)