logo

HAUSA

Shugaba Putin ya dora alhakin harin gadar Crimean kan Ukraine

2022-10-10 11:40:27 CMG Hausa

Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya bayyana harin da aka kai wa gadar Crimea a ranar Asabar, a matsayin aikin ta’addanci.

Wata sanarwar da fadar Kremlin ta fitar jiya ta ce, yayin da shugaba Putin yake ganawa da Alexander Bastrykin, shugaban kwamitin bincike na kasar, ya zargi jami’an leken asiri na Ukraine da shirya harin. Yana mai cewa su ne suka shirya, suka kitsa tare da aiwatar da shi.

A cewar Alexander Bastrykin, jami’an tsaro na farin kaya na Rasha za su taimaka wajen gano mutanen da ake zargi, ciki har da wadanda ke zaune a cikin kasar. Ya kara da cewa, jami’an leken asiri na Ukraine da ’yan kasar Rasha da na kasashen waje ne suka taimaka wajen kai harin.

Sai dai Ukraine ba ta yi tsokaci game da zargin ba.

Harin ya auku ne a ranar Asabar kan gadar Crimean mai tsawon kilomita 19, wanda ya kunshi hanyar mota da ta jirgin kasa, a zirin Kerch. (Fa’iza Mustapha)