logo

HAUSA

Girman kan Amurka ya sake fuskantar koma baya

2022-10-10 20:08:06 CMG Hausa

Da yake mai da hankali kan shawarar "OPEC+" ta rage yawan danyen man da ake hakowa a kowace rana da ganga miliyan 2 daga watan Nuwamba, kuri’ar jin ra'ayin jama’a a Amurka ta kara nuna fushin ‘yan kasar a 'yan kwanakin nan.

Da farko dai gwamnatin Biden ta yi fatan manyan kasashen da ke hako mai a yankin Gabas ta Tsakiya, za su kara yawan man da suke hakowa don magance tashin farashin mai da kuma taimakawa Amurka wajen shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyakin da take fuskanta, amma abin ya ci tura.

Jaridar "Capitol Hill" ta yi sharhi cewa, shawarar "OPEC+" ta raunata manufar Biden game da harkokin kasashen waje. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)