logo

HAUSA

Putin ya ba da umarnin tsaurara matakan kare sassan dake da alaka da Crimea

2022-10-09 16:18:32 CMG Hausa

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya sanya hannu kan wata doka a jiya Asabar, a wani mataki na karfafa matakan kare harkokin zirga-zirgar ababan hawa ta mashigin Kerch, dake zama tashar wutar lantarki da ta hada Crimea da bututun iskar gas zuwa mashigin teku.

Wata sanarwa da fadar Kremlin ta fitar ta bayyana cewa, shugaba Putin ya baiwa hukumar tsaro ta tarayyar Rasha umarnin tsarawa da daidaita matakan kare wadannan wurare yadda ya kamata..

Tun da farko a jiya Asabar, wata fashewa mai muni ta auku a gadar Crimea mai nisan kilomita 19, wadda ta kunshi hanyoyi guda 2 da motoci da jiragen kasa ke bi a kan mashigin na Kerch.

Wata motar dakon kaya ce ta yi bindiga a kan gadar, inda tankuna mai guda 7 na wani jirgin dake kan hanyar zuwa yankin Crimea ya kama da wuta. Mutane uku ne aka ba da rahoton sun mutu sakamakon fashewar, wanda kuma ya kai ga rugujewar wani sashe na hanyar gadar.

An sake bude harkokin zirga-zirgar ababan hawa ga kananan motoci da bas-bas tare da cikakken tsari na bincike, yayin da ake bukatar manyan motoci da su tsallaka mashigin Kerch ta jirgin ruwa, a cewar shugaban yankin Crimea Sergei Aksyonov.

Firaministan kasar Rasha Marat Khusnullin ya bayyana a yammacin jiya cewa, a halin da ake ciki dai, an sake dawo da aikin layin dogo a kan gadar, kuma dukkan jigaren kasa da aka tsara na fasinjoji da jigilar kaya, za su iya tsallakawa ta hanyar ba tare da wata matsala ba. (Ibrahim)