logo

HAUSA

Jami’in MDD: Tashin hankalin da ya barke a yammacin kogin Jordan na iya haifar da fargaba da kiyayya

2022-10-09 16:14:33 CMG Hausa

Babban jami’in MDD na musamman kan shirin samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya Tor Wennesland ya yi gargadin cewa, karuwar tashe-tashen hankula a gabar yammacin kogin Jordan, za su iya haifar da yanayi na tsoro da kiyayya da fushi tsakanin Yahudawan Isra’ila da Falasdinawa.

Tor ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya aikewa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, ya zama tilas a rage zaman dar-dar ba tare da bata lokaci ba, domin bude hanyar samar da kyakkyawar fahimta ta siyasa a tsakamnin sassan biyu.

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta bayyana cewa, a ranakun Jumma’a da Asabar da suka gabata, sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa 4 tare da jikkata wasu da dama a garuruwa da kauyuka da dama a gabar yammacin kogin Jordan.

A cewar ma’aikatar, tun a farkon watan Janairu, sama da Falasdinawa 100 ne sojojin Isra’ila suka kashe. Daga watan Maris zuwa yanzu kuwa, an kashe ‘yan Isra’ila 18 a wasu hare-hare da Falasdinawa suka kai a garuruwan Isra’ila.

Wennesland ya bayyana damuwarsa kan tarbarbarewar harkoki na tsaro a yammacin kogin Jordan da gabashin birnin Kudus, inda ya yi kira ga al’ummar Isra’ila da falasdinawa, da su kwantar da hankula tare da kaucewa kara tabarbarewar yanayin tsaro. (Ibrahim)