logo

HAUSA

Kudurin majalisar kare hakkin bil Adama ta MDD ta yi kira da kasashe masu ruwa da tsaki da su shawo kan nuna rashin adalci bisa wariyar launin fata

2022-10-08 21:00:13 CMG Hausa

 

A jiya Juma’a ne, zaman taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 51, ya amince da kudurin da ya bukaci kasashe masu ruwa da tsaki, da su shawo kan rashin adalci da aka tafka bisa tushen wariyar launin fata a tarihi, ta yadda hakan zai taimaka wajen dawo da martabar al’ummu da kasashen da abun ya shafa.

Kudurin mai taken "Daga cece-kuce zuwa gaskiya: Kira ga sassan kasa da kasa, game da daukar kwararan matakan yaki da wariyar launin fata, da nuna kyamar wasu al’ummu, da sauran ayyuka na nuna kiyayya", ya bayyana yadda wasu kasashe suka dauki matakan neman afuwa, da biyan diyya bisa muggan ayyukan da suka tafka sakamakon cinikin bayi, da shi kan shi cinikin bayin, da mulkin mallaka, da nuna kyamar babaken fata, da kisan kiyashi, da sauran muggan laifuka da aka aikata a tarihi. Kudurin ya kara da cewa, ya kamata sassan da ba su nuna nadama ba, ko suka ki neman afuwa su nemi wasu hanyoyi, na dawo da kimar wadanda tozartawar ta shafa.

Yayin da kudurin ya yi tir da yawaitar amfani da karfi fiye da kima, da sauran nau’o’in keta hakkin bil Adama da jami’an tsaro ke aikatawa a wasu kasashe, ya kuma jaddada muhimmancin dake akwai ga wadannan kasashe, na su tabbatar da biyan diyya ga wadanda aka ci zarafin su, tare da tabbatar da ‘yancin su, da gaggauta gudanar da bincike kan hakan.  (Saminu Alhassan)