logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya na bincike game da musabbabin aukuwar gobara a wasu rijiyoyin mai

2022-10-05 16:11:18 CMG Hausa

 

Gwamnatin kasar Najeriya ta ce ta kaddamar da bincike, game da musabbabin aukuwar gobara a wasu rijiyoyin mai guda 2, dake jihar Rivers mai arzikin man fetur.

Shugaban hukumar dake lura da kwararar mai da shawo kan hakan ko NOSDRA a takaice Idris Musa, ya fitar da wata sanarwa a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, inda ya ce sun samu rahoton tashin gobara a rijiyoyin hakar mai na Akaso 14, da 4T Wellheads, muhimman rijiyoyin mai biyu da babban kamfanin Eroton ke aikin hakar mai a cikin su.

Musa ya kara da cewa, ba a kai ga kashe wutar da ta tashi ba, amma ana kokarin hakan, kuma suna musayar bayanai duk sa’o’i 2, tsakanin su da kamfanin dake aikin hakar mai a rijiyoyin, da sauran sassa masu ruwa da tsaki kan wannan lamari.

Jami’in ya ci gaba da cewa, sun samu rahoton hango wani kwale-kwale dake yunkurin satar mai a yankin da lamarin ya auku, wanda ya kone kurmus, an kuma yi nasarar kashe wutar dake ci a cikin sa.  (Saminu Alhassan)