logo

HAUSA

Jakadan Sin Ya Yi Kira Ga Kasashe Masu Ruwa Da Tsaki Da Su Bincika Tare Da Daukar Matakan Doka Kan Wadanda Suke Keta Hakkokin Yara ‘Yan Asalin Afirka

2022-10-04 17:10:12 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a ofishin MDD dake birnin Geneva Chen Xu, ya yi kira ga kasashe masu ruwa da tsaki, da su bincika, tare da daukar matakin doka, kan sassan da suke keta hakkokin yara ‘yan asalin Afirka, ta yadda yara ‘yan asalin Afirka za su samu damar yin ingantacciyar rayuwa. Chen Xu ya ce al’ummu ‘yan asalin Afirka, da wadanda suka fito daga nahiyar, sun shafe tsawon lokaci suna fuskantar muzgunawa karkashin laifukan wariyar launin fata da nuna kyama.

Jami’in na kasar Sin ya bayyana hakan ne, yayin taron tattaunawa tsakanin kwararru daga MDD, dake ayyukan da suka shafi nazartar halin da al’ummu ‘yan asalin Afirka ke ciki, da ‘yan tawagar taron hukumar kare hakkin bil Adama ta MDD karo na 51.

Chen Xu, ya kara da cewa, yara ‘yan asalin Afirka na cikin yanayi na fuskantar barazana, da wahalhalu, da cutarwa mai tarin yawa. Kana sau da yawa suna fama da ayyukan karfi, da fatara, da barazanar harbin bindiga a makarantu da sauran hadurra, yayin da kuma suke fuskantar keta hakkin su na bil aAdama, da ‘yancin rayuwa.

Chen ya jaddada cewa, kasar Sin ta amince da shawarwarin da aka sanya cikin rahoton rukunin masu aikin na MDD, tana kuma kira ga sassan kasa da kasa, da su rattaba hannu kan yarjejeniyar kare hakkin yara, su kuma sake yin cikakken nazari game da dokoki da manufofin kasashen su, su haramta duk wasu matakai, da manufofi dake da illa ga al’ummu masu asali daga Afirka, su kuma magance duk wani tsari na nuna wariyar launin fata.  (Saminu Alhassan)