logo

HAUSA

Wakilin Sin ya kalubalanci Amurka da ta daidaita matsalar nuna bambancin launin fata a ayyukan ‘yan sanda da sauransu

2022-10-04 17:02:57 CMG Hausa

Wakilin Sin Jiang Duan, ya shaidawa taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 51 da aka gudanar a jiya cewa, ‘yan asalin Afirka dake Amurka, suna fuskantar yanayin nuna bambanci a ayyukan aiwatar da doka, don haka ya kalubalanci kasar Amurka, da ta dauki matakai don daidaita matsalolin nuna bambancin launin fata, da tsauraran matakan da ‘yan sanda suke dauka bisa bambacin launin fata da sauransu.

Jiang Duan ya yi nuni da cewa, ra’ayin mulkin mallaka, da cinikin bayi, sun haifar da ra’ayin nuna bambancin launin fata. Ko da yake wannan babi ya wuce a tarihin dan Adam, amma ra’ayin mayar da fararen fata a gaban wasu yana ci gaba da kasancewa. Ya ce a kasar Amurka, ‘yan asalin Afirka suna fuskantar yanayin nuna bambancin launin fata, da rashin daidaito gare su.

Bisa kididdigar da aka yi, yiwuwar samun mutanen ‘yan asalin Afirka da ‘yan sanda suke harbewa har lahira, ta fi ta fararen fata fiye da ninki biyu, kana yawan ‘yan asalin Afirka da suke cikin kurkuku a kasar Amurka, ya fi na fararen fata har ninki shida.

Jiang Duan ya bayyana cewa, kasar Sin ta kalubalanci kasar Amurka, da ta dauki matakai, don daidaita matsalolin nuna bambancin launin fata, da tsauraran matakan da ‘yan sanda suke dauka bisa bambancin launin fata da sauransu, da aiwatar da kudurin da aka tsai da a babban taron MDD, da majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD. (Zainab)