logo

HAUSA

Ba wani mai hakkin hawa kujerar naki game da makomar falasdinu in ji wakilin kasar Sin

2022-09-29 11:39:23 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya jaddada muhimmancin tabbatar da daidaito da adalci game da batun Falasdinawa. Yana mai cewa, ba wani mai hakkin hawa kujerar naki, game da makomar Falasdinawa.

Zhang, wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin taron kwamitin tsaron MDD, ya ce kamata ya yi majalissar ta sauke nauyin dake wuyanta na kare gaskiya, da kawar da son kai, daidai da manufofin kasa da kasa masu nasaba da hakan. Kazalika ta goyi bayan gaggauta komawa teburin shawara tsakanin tsagin Falasdinu da na Isra’ila, a maimakon jiran cikar wasu sharudda na komawa shawarwarin.

Jami’in ya ce hanya daya tilo ta tabbatar da nasarar warware rikicin sassan biyu, ta ta’allaka ne ga kafuwar kasashen Falasdinu da Isra’ila masu cin gashin kansu. A cewarsa tuni kasashen duniya suka amince da hakan, a matsayin ginshikin wanzar da gaskiya da adalci, don haka ya dace, kowa rungumi hakan ba tare da jan kafa ba. (Saminu Alhassan)