logo

HAUSA

Sin ta yi kira ga Amurka da Canada da Austriliya da su duba matsalarsu ta nuna wariya ga ‘yan asalin wurin

2022-09-29 10:17:29 CMG HAUSA

 

Wakilin kasar Sin ya ba da jawabi a gun taron tattauna kan hakkin ‘yan asalin kasashe, a taron kwamiti mai kula da hakkin bil Adama karo na 51 na MDD a jiya Laraba, inda ya yi kira ga gwamnatocin Amurka, da Canada da Austriliya, da su yi tunani mai zurfi, su duba matsalarsu ta nuna wariya ga ‘yan asalin yankunan kasashensu.

Wakilin na Sin ya ce, bisa nazarin da aka yi, ‘yan asalin Amurka na fuskantar matsaloli guda 11 a fannin shiga ayyukan siyasa. A halin yanzu kuma, Indiyawan dajin ‘yan asalin Amurka, ba su da ikon ba da gudunmawarsu a fannin siyasa kamar sauran Amurkawa ba. Ban da wannan kuma, an gano dumbin kaburburan yara ‘yan asalin Canada da ba a san ko su waye ba.

Kazalika, yawan ‘yan asalin kasar Austriliya da ake tsare da su, ya zarce na wadanda ba ‘yan asalin kasar ba yawa da ninki har 15. Ban da wannan kuma, yawan ‘yan asalin kasar wadanda ke mutuwa a cikin gidan kurkuku shi ma yana karuwa matuka. (Amina Xu)