logo

HAUSA

Jam'iyyun siyasa a Najeriya na shirin fara yakin neman zabe gabanin babban zaben 2023

2022-09-29 11:36:08 CMG Hausa

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta baiwa jam'iyyun siyasa da aka yiwa rijista a kasar, damar kaddamar da yakin neman zabensu, gabanin babban zaben da za a yi a watan Fabrairu mai zuwa a kasar dake zama mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.

A yayin da jam’iyun siyasan ke shirin fara kamfel ko yakin neman zabe, ’yan takarar shugaban kasa 18 ne za su fafata neman kuri’u a jihohi 36 na Najeriya. Kuma dukkan jam'iyyun siyasar kasar da manyan 'yan takararsu, na da a kalla kwanaki 147 ko sama da watanni 4, su karade sassan kasar, domin neman goyon bayan masu zabe.

Hukumar zaben kasar ta tsayar da ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023, domin gudanar da zabukan shugaban kasa da na ’yan majalisun tarayya, yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni da na ’yan majalisun jihohi bayan mako guda.

Bayanan da hukumar zaben ta fitar a watan Agustan na nuna cewa, kimanin masu kada kuri’a 84,004,084 ne hukumar ta yi wa rijista, don shiga zaben dake tafe.

Da yake jawabi a ranar Talata a wani taron da aka yi a Abuja, babban birnin Najeriyar, shugaba Muhammadu Buhari ya ce, za a gudanar da zaben shekarar 2023 bisa gaskiya da adalci. (Ibrahim Yaya)