logo

HAUSA

Kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin raya karkara cikin shekaru 5 da suka gabata

2022-09-29 11:37:00 CMG Hausa

Babban jami’in tsara tattalin arzikin kasar Sin, ya bayyana cewa, kasar ta samu ci gaba mai inganci a fannin ciyar da ayyukan raya yankunan karkarar kasar gaba, kamar yadda aka tsara a cikin shekaru biyar da suka gabata.

A shekarar 2018, kasar Sin ta fito da wani shiri game da raya yankunan karkara na tsawon shekaru biyar, inda ta tsara wasu manyan ayyuka, da shirye-shirye gami da managartan matakai.

Jami’in hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Wu Xiao, ya shaidawa taron manema labarai cewa, dukkan muhimman ayyuka dake kunshe cikin shirin, wadanda suka hada da kara karfin samar da yawan amfanin gona, da inganta samar da ruwan sha mai tsafta a yankunan karkara, an aiwatar da su yadda ya kamata tare da samun sakamako mai kyau.

Wu ya bayyana cewa, daga shekarar 2017 zuwa shekarar 2021, kudaden da kowane zamaunin karkaka yake samu, ya karu da