logo

HAUSA

Kasar Sin ta bukaci a dauki matsaya na adalci kan kungiyar Taliban ta Afghanistan

2022-09-28 20:01:29 CMG Hausa

 

Wani jami'in kasar Sin ya bukaci kasashen duniya, da su dauki matsaya na hakika kan 'yan Taliban na kasar Afghanistan, yana mai cewa, ana kokarin dawo da zaman lafiya a kasar.

A wani taron manema labarai da aka saba shiryawa, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, shi ma ya yi na’am cewa, a halin yanzu kasar Afghanistan na cikin wani muhimmin lokaci da za ta sauya daga yanayi na rudani zuwa yanayi mai tsari, inda har zuwa wannan lokaci ba a kai ga kawar da barazanar 'yan ta'adda a kasar ba.

Wang ya kuma yi kira ga kasa da kasa, da su ci gaba da yin mu’amala da gwamnatin wucin gadin kasar Afghanistan, da kara samar da taimakon jin kai da raya kasa ga kasar, yana mai jaddada kiyaye hakkin dukkanin al’ummar kasar, musamman ma dukkan kananan kabilu, da mata da kananan yara dake kasar. (Ibrahim)