logo

HAUSA

Shawarar “ziri daya da hanya daya” za ta karfafa alakar tattalin arzikin Afirka da Sin

2022-09-27 11:25:56 CMG Hausa

Wani dan majalisar dokokin kasar Rwanda ya bayyana cewa, shawarar “ziri daya da hanya daya (BRI)” za ta inganta hadin gwiwar cinikayya da zuba jari tsakanin Sin da kasashen Afirka, da zarar an magance kalubalen cudanya da sufuri da ake fuskanta.

A wata hirar da aka yi da shi kwanan nan a Kigali, babban birnin kasar, shugaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje, hadin gwiwa da tsaro a majalisar wakilan kasar Emmanuel Bugingo ya ce, shawarar “ziri daya da hanya daya”, za ta cike gibin ababen more rayuwa da ake fuskanta a kasar Rwanda, ta yadda za a hade kasar da sassan nahiyar da ma duniya baki daya.

Ya bayyana cewa, ana iya ganin sakamakon hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka cikin shekaru da dama da suka gabata a fannin aikin gona. Wasu alkaluman da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a bara, yawan kayayyakin amfanin gona na Afirka aka shigar cikin kasar Sin, ya karu da kashi 18.2 cikin 100 bisa makamancin lokacin shekarar 2020.

Ya bayyana cewa, kasar Rwanda ta yaba da gudummawar da kasar Sin take bayarwa wajen gina ababen more rayuwa a kasar da ma Afirka baki daya.

Game da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Rwanda da Sin kuwa, Bugingo ya ce, tana gudana ne bisa la’akari da mutunta juna da dabi’unsu da kare muradun juna.

Bugingo ya kuma lura cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Rwanda da Sin a fannin yaki da cutar COVID-19, ta kara kusanto da ma kara karfin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ya kuma yabawa tsarin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka daban-daban, wanda ya ce, ya dogara ne kan mutunta juna. (Ibrahim)