logo

HAUSA

An bude bikin baje kolin tsaro da jiragen sama na Afirka na 2022 a Afirka ta Kudu

2022-09-22 10:15:59 CMG Hausa

A jiya ne, aka bude bikin baje kolin harkokin sararin samaniya da tsaro na kasashen Afirka na shekarar 2022 (AAD) a sansanin sojojin sama na Waterkloof dake Pretoria na kasar Afirka ta Kudu.

Bikin baje kolin na AAD zai gudana ne har zuwa ranar Lahadi, inda aka kebe kwanaki uku na farko a matsayin ranakun kasuwanci, yayin da ranaku biyu na karshe ke zama na nunin jiragen sama.

Da yake yi wa manema labarai karin haske kan bikin na AAD 2022, ministan tsaron kasar Thandi Modise ya bayyana cewa, taron zai ba da damar yin aiki tare ga kamfanoni daga sassan duniya. Kasashen Amurka, da Italiya, da Turkiyya, da Belgium, da Sin, da Birtaniya, da Indiya, da Pakistan na daga cikkin wadanda za su halarci taron.

A cewar masu shirya bikin, za a gudanar da nune-nunen jiragen sama a ranar 24 da 25 ga watan Satumba, a sansanin sojojin sama na Waterkloof dake Pretoria, baya ga wasanni da jiragen sama a sararin samaniya da aka shirya cikin jerin shagulgulan da za a gudanar a bikin na bana.

A yayin taron, rundunar sojojin tsaron Afirka ta Kudu za ta tsara wani shiri na "karamin yaki", yayin da hukumar 'yan sandan kasar kuma, za ta shirya wani shirin kwato mutanen da aka yi garkuwa da su, dukkansu za a yi amfani da jiragen sama, da motoci, da ma harbin bindiga. (Ibrahim Yaya)