logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira ga bangarori daban daban da su aiwatar da shawarar tsaron kasa da kasa a majalisar kare hakkin bil’adam

2022-09-20 14:09:21 CMG Hausa

Wakilin Sin ya yi jawabi a taron majalisar kare hakkin bil’adam karo na 51 da kuma taron tattaunawar masana masu zaman kansu a kan tsarin mulkin duniya bisa dimokuradiyya da adalci da aka gudanar a zauren majalisar kare hakkin bil’adam a jiya Litinin. Yayin taron, ya yi kira ga bangarori daban daban da su aiwatar da shawarar tsaron kasa da kasa, da aiwatar da ra’ayin bangarori daban daban.

Wakilin Sin ya bayyana cewa, ra’ayin bangarori daban daban, babban ra’ayi ne a tsarin duniya da kuma tsarin mulkin duniya. Kuma ita ce hanyar kare zaman lafiya da kuma inganta ci gaba. A cewarsa, kamata ya yi al’ummar duniya ta kare da kuma aiwatar da ra’ayin bangarori daban daban bisa gaskiya, da adawa da ra’ayin danniya da kuma siyasar rukunoni tare kuma da adawa da takunkuman da wani bangare daya ke kakkabawa.

Har ila yau, ya bayyana cewa, bangaren Sin ya fitar da shawarar tsaron kasa da kasa, kuma ya gabatar da dabara don warware gibin zaman lafiya da magance matsalar tsaro a duniya. Yana mai cewa ita ce shawarar tsaron al’umma da Sin ta samar wa duniya. Haka kuma, ya ce kamata ya yi kasa da kasa su tattaunawa da juna a maimakon nuna adawa, kuma su yi mu’ammala da juna a maimakon barazana, sannan su maye gurbin adawa da zumunci da maye gurbin nasarar gefe daya da samun nasara tare. Haka kuma, su aiwatar da ka'idar rashin rarrabuwar kawuna, da dora muhimmanci kan matsalolin tsaro na juna, da habaka gina tsarin gine-ginen tsaro masu inganci da dorewa. Bugu da kari, ya ce kasar Sin tana son hada hannu da sauran kasashen duniya wajen kiyaye dabi'u guda na zaman lafiya, da samun ci gaba, da tabbatar da adalci, da dimokuradiyya, da 'yanci ga dukkan bil'adam, da aiwatar da ra'ayin jama'a na hakika, da aiwatar da ayyukan tabbatar da tsaron duniya, da sa kaimi ga gina al'umma mai makoma ta bai daya ga bil'adam. (Safiyah Ma)