logo

HAUSA

Wang Yi ya bukaci Amurka da ta fuskanci batun Taiwan yadda ya kamata

2022-09-20 20:54:38 CMG Hausa

Dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira ga mahukuntan Amurka, da su fuskanci batun da ya shafi yankin Taiwan na kasar Sin bisa adalci, domin kaucewa tabarbarewar alakar Sin da Amurka. Wang Yi ya yi wannan tsokaci ne a jiya Litinin, yayin zantawarsa da tsohon sakataren wajen Amurka Henry Kissinger a birnin New York.

Mr. Kissinger, wanda ke cikin jami’an da suka cimma sanarwar Shanghai, tsakanin tsagin Sin da na Amurka shekaru 50 da suka gabata, ya yi bitar yadda shi da shugabannin Sin na wancan lokacin, suka cimma matsaya mai cike da tarihi, yana mai cewa, ya kamata a martaba hakkin Sin game da batun Taiwan.

Kissinger ya kara da cewa, ya kamata Sin da Amurka su rungumi tattaunawa maimakon fito na fito, su kuma gina kyakkyawar alaka cikin lumana.

A wani ci gaba kuma, Wang Yi ya jaddada bukatar yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka, a fannin wanzar da kyakkyawar dangantaka. Wang ya bayyana hakan ne, yayin zantawar sa da wakilai daga kwamitin kula da alakar Amurka da Sin, da majalissar kula da harkokin kasuwanci tsakanin Amurka da Sin, da wakilai daga cibiyar raya kasuwanci ta Amurka, a gefen babban taron MDD dake gudana a birnin New York.

Yayin taron, Wang ya fayyace aniyar kasar Sin ta zurfafa gyare gyare da kara bude kofa ga waje. Kaza lika ya jaddada muhimmancin wanzar da ginshikin alakar Sin da Amurka ta fannin siyasa, musamman ma batun da ya shafi manufar nan ta kasancewar Sin daya tak a duniya. (Saminu Alhassan)