logo

HAUSA

Hanyar da kasar Sin ta gina ya saukaka zirga-zirga a Rwanda

2022-09-19 11:04:46 CMG Hausa

Wani aikin gyaran titi da Rwanda ta bada kwangilarsa ga kamfanin gine-gine na CRBC na kasar Sin, ya taimaka wajen saukaka zirga-zirgar da inganta cinikayya a kan hanyar Kigali zuwa Bugesera dake gabashin Rwanda.

Titin mai tsawon kilomita 13.8, ya fara ne daga Shatale-talen Sonatube dake Kigali, babban birnin kasar, ya ratsa ta yankin Gahanga, zuwa gadar Akagera dake gundumar Bugesera. Haka kuma, wani bangare ne na hanyar dake kai wa sabon filin jirgin saman kasa da kasa na Bugesera dake da nisan kilomita 40 daga kudancin filin jirgin saman kasa da kasa na Kigali.

Kamfanin CRBC wanda ya fara gyaran titin a shekarar 2019, ya kuma dauki sama da shekaru 3 kafin ya kammala saboda wasu dalilai kamar na annobar COVID-19, ya samu yabo daga mutanen yankin, saboda yadda titin ya saukaka zirga-zirgar ababen hawa da na mutane da kayayyaki, tare da inganta ci gaban tattalin azikin yankin babban titin na Kigali zuwa Bugesera.

Wani dan kasuwa dake bin titin, Emmaneul Habineza, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, kafin gyara titin, su kan sha wahala saboda cunkoson ababen hawa, musamman a tsakiyar garin Kicukiro, saboda hannaye biyu kadai titin ke da shi, kana ba shi da fadi. Ya ce mutanen dake tafiya garin Nyamata na yankin Bugesera daga Kigali ne suka fi bin titin, kuma galibinsu na bin hanyar ne a kullum.