logo

HAUSA

Adadin jarin waje da Sin ta samu a watanni 8 na farkon bana ya kai yuan biliyan 892.74

2022-09-19 20:20:19 CMG Hausa

Alkaluman da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a cikin watanni 8 na farkon shekarar bana, wato tsakanin watan Janairu zuwa Agusta, adadin jarin waje da ake amfani da shi a fadin kasar Sin, ya kai kudin Sin yuan biliyan 892.74, adadin da ya karu da kaso 16.4 bisa dari, idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara, kuma daga cikin adadin, jarin wajen da ake amfani da shi a sana’o’in fasahohin zamani, ya karu da kaso 33.6 bisa dari.

Kakakin watsa labarai na hukumar raya kasa da yin kwaskwarima Meng Wei, ta bayyana cewa, “Tun daga farkon bana, adadin jarin waje da ake amfani da shi a kasar Sin ya karu cikin sauri, a cikin sa, adadin jarin waje da ake amfani da shi a sana’o’in fasahohin zamani ya fi saurin karuwa, kuma adadin da ake amfani da shi a yankin tsakiya, da yamma, ya fi na yankin gabas, kana tsarin zuba jari na ‘yan kasuwar ketare ya kyautata, yayin da na kasashen Amurka, da Jamus, da Koriya ta kudu suka fi rinjaye, a bangaren karuwar zuba jari a kasar Sin.” (Jamila)