logo

HAUSA

Xi da takwaransa na Togo sun taya juna murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashensu

2022-09-19 18:56:28 CMG Hausa

A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Togo Faure Essozimna, suka aikewa juna sakon taya murnar cika shekaru 50, da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashensu, inda cikin sakon sa shugaba Xi ya bayyana cewa, akwai dadadden zumuncin gargajiya tsakanin Sin da Togo, kuma duk da cewa, yanayin duniya yana sassauyawa a cikin shekaru 50 da suka gabata, amma a ko da yaushe sassan biyu na ci gaba da goyawa juna baya, kan batutuwan dake shafar babbar moriyarsu, da al’amuran dake jawo hankalinsu, don haka hadin gwiwar dake tsakaninsu ya samu babban sakamako, ta yadda yake amfanar al’ummun kasashen biyu baki daya.

Ya ce yanzu haka ana fuskantar matsalar yaduwar annobar cutar COVID-19 a fadin duniya, don haka ya dace al’ummun kasashen biyu su kara hada kai domin dakile annobar, tare kuma da kara zurfafa zumuncin dake tsakaninsu yadda ya kamata. Shugaba Xi ya kara da cewa, yana mai da hankali matuka kan ci gaban huldar dake tsakanin kasarsa da kasar Togo, yana kuma son yin kokari tare da takwaransa na kasar Faure Essozimna, a yayin da ake taya juna murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya dake tsakanin kasashen biyu, domin kara karfafa amincin siyasa, da hadin gwiwa a fannoni daban daban tsakaninsu, tare kuma da ciyar da huldar sassan biyu gaba, da taka rawa a fannin gina kyakkyawar makomar al’ummun Sin da Afirka bai daya.

A nasa bangare, shugaba Faure ya yi tsokaci da cewa, har kullum kasar Sin aminiyar kasar Togo ce, yayin da take kokarin raya kan ta, kuma yana farin cikin ganin yadda kasar Sin din ke yin kokari tare da kasashen Afirka, wajen kara karfafa huldar dake tsakaninta da kasashen Afirka, ta yadda za su samu wadata tare.

Ya kara da cewa, kasar Togo tana nacewa, kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, yana kuma son yin kokari tare da shugaba Xi, wajen ciyar da huldar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin gaba yadda ya kamata. (Jamila)