logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 145 a jamhuriyar Nijar

2022-09-18 17:01:57 CMG Hausa

Ma’aikatar dake kula da harkokin cikin gida a jamhuriyar Nijar, ta sanar da jiya Asabar cewa, ambaliyar ruwa ta haddasa rasa rayukan mutane 145 a kasar, yayin da iftila’in ya ritsa da jimillar mutane fiye da dubu 210.

Sanarwar ta ce, an dade ana samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a wurare daban daban na Nijar, tun daga watan Yuni har zuwa yanzu, lamarin da ya haddasa ambaliyar ruwa, wadda ta sa dimbin gidaje rushewa, da haifar da babbar hasara ga ayyukan kiwon dabbobi, da na noma.

Rahotanni sun ce mazauna jahohin Maradi da Zinder dake kudancin kasar ne suka fi fuskantar radadin iftila’in. (Bello Wang)