logo

HAUSA

Xi ya dawo birnin Beijing bayan halartar taron kolin SCO da ziyartar Kazakhstan da Uzbekistan

2022-09-17 16:26:09 CMG Hausa

Jiya da dare ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dawo birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, bayan kammala halartar taron majalisar shugabannin kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) karo na 22, tare da kai ziyarar aiki a kasashen Kazakhstan da Uzbekistan.

A yammacin jiya agogon kasar Uzbekistan, Xi ya kama hanyar zuwa filin jiragen sama kai tsaye, bayan kammala halartar taron SCO a Samarkand, fadar mulkin kasar. Shugaban kasar Uzbekistan Shavkat Mirziyoyev ne ya yi ban kwana da shi a wajen dakin taron, yayin da firaminista Abdulla Aripov ya yi ban kwana da shi a filin jiragen sama.(Ibrahim)