logo

HAUSA

Xi ya yi kira ga kasashen SCO da su zurfafa hadin gwiwa da ciyar da ruhun Shanghai gaba

2022-09-16 19:04:32 CMG Hausa

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) da su ci gaba da tafiyar da kungiyar bisa tafarkin da ya dace wajen samun bunkasuwa da farfado da kasashe mambobin kungiyar.

Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya halarci takaitaccen zaman taron majalisar shugabannin kasashen kungiyar SCO karo na 22.

A yayin jawabin nasa, Xi ya yi kira ga kasashe mambobin kungiyar SCO, da su ci gaba da tabbatar da ruhin Shanghai, da inganta hadin kai da hadin gwiwa, da kiyaye 'yancin kai bisa manyan tsare-tsare, da kiyaye zaman lafiya a yankin, da damawa da kowa da samun moriyar juna, wajen sa kaimi ga hadin gwiwar raya kasa, da ciyar da tsarin fadada kungiyar ta SCO, da karfafa hadin gwiwar cibiyoyin kungiyar. (Ibrahim)