logo

HAUSA

Za a wallafa sharhin da Xi ya rubuta game da kiyayewa da bunkasa tsarin gurguzu mai sigar musamman na Sin

2022-09-15 19:04:08 CMG Hausa

Gobe Juma'a ne, za a wallafa sharhi kan batutuwan da suka shafi kiyayewa da raya tsarin gurguzu mai sigar musammman na kasar Sin, da Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS (CPC) ya rubuta.

Zai dai a wallafa sharhin da Xi, wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin kana shugaban kwamitin koli na soja ya rubuta ne, a mujallar Qiushi ta bana karo na 18, mujallar kwamitin kolin JKS. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)