logo

HAUSA

Sin na adawa da takunkuman kashin kai da Amurka da kasashen yamma suka kakaba mata a zaman MDD

2022-09-15 19:46:20 CMG Hausa

Kasar Sin ta nuna adawa da takunkuman kashin kai da suka saba doka da Amurka da wasu tsirarun kasashen yammacin duniya suka kakaba mata a yayin taron hukumar kare hakkin bil adama ta MDD karo na 51 (UNHRC) da aka gudanar a birnin Vienna.

A cewar wakilin kasar Sin a tattaunawar da wakilin musamman na MDD kan takunkuman kashin kai, irin wadannan takunkumai na kashin kai da sassan ke kakabawa kasashe, sun saba dokokin kasa da kasa. (Ibrahim)