logo

HAUSA

Kasar Sin: an gudanar da taron baje kolin zuba jari da cinikayya na kasa da kasa karo na 22 cikin nasara

2022-09-14 20:30:26 CMG Hausa

Kwanan baya, an gudanar da taron baje kolin zuba jari da cinikayya na kasa da kasa karo na 22 cikin nasara, inda aka cimma dimbin sakamako da yawa. Mao Ning, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau 14 ga wata cewa, gudanar da taron cikin nasara ya sake nuna yadda kasar Sin take kokarin bude kofa ga waje da yin hadin gwiwa da kasashen waje, da kuma shiga kasuwannin duniya.