logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya jaddada bukatar aiwatar da manufofin daidaita tattalin arziki

2022-09-13 14:02:27 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada bukatar aiwatar da manufofin daidaita tattalin arziki, da farashin kayayyaki, da samar da guraben ayyukan yi.

Li ya yi tsokacin ne yayin taron majalissar gudanarwar kasar Sin, bayan da ya saurari rahotanni daga tawagogin aikin daidaita sassan tattalin arziki guda 2. Ya ce daidaituwar tattalin arziki ya danganta da yanayin hada-hadar kasuwanni, don haka ya bukaci a kara azama, wajen rage wahalhalun da sashen hada hadar kasuwannin ke fuskanta, yayin da ake kara fadada harkokin zuba jari, har a kai ga samar da damammakin bunkasa kasuwanni, da karfafa kwarin gwiwar su.

Li Keqiang ya ce ya dace a kara azama wajen kammala manyan ayyuka, da fadada hada-hadar kudade bisa tsare-tsare da aka tanada gwargwadon bukatun gida.

Ya ce gwamnati za ta tallafawa bukatun al’umma na samun muhalli, da kyautata muhallin al’umma, da yin kyakkyawan amfani da manufofi, ta hanyar aiwatar da manufofi mafiya dacewa da birane daban daban.  (Saminu Alhassan)