logo

HAUSA

Ziyarar Xi ita ce muhimmin aikin diflomasiyya da shugaban ya yi a jajibirin taron wakilan JKS karo na 20

2022-09-13 18:58:18 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta gabatar da cewa, shugaba Xi Jinping zai halarci taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, zai kuma kai ziyara a kasashen Kazakhstan da Uzbekistan.

Ta bayyana cewa, wannan ziyara shi ne muhimmin aikin diflomasiyya da shugaban kasar Sin ya gudanar a gabanin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, wanda ke nuna cikakken muhimmancin da bangaren Sin yake dorawa kan kungiyar SCO da alakar kasar Sin da Uzbekistan da kuma Kazakhstan. (Ibrahim)