logo

HAUSA

MDD ta lashi takobin goyon bayan wadanda ayyukan ta’addanci ya shafa

2022-09-10 17:09:28 CMG Hausa

Taron kasa da kasa kan mutanen da ayyukan ta’addanci ya shafa na MDD da aka kammala jiya a hedkwatar majalisar dake birnin New York, ya yi alkawarin karfafa goyon baya ga mutane masu ruwa da tsaki.

Ofishin MDD mai yaki da ta’addanci, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, manufar taron mai taken “inganta hakkoki da bukatun wadanda ayyukan ta’addanci ya shafa” ita ce, daukar matakin da zai mayar da hankali kan mutanen, wajen yaki da ta’addanci da ra’ayi mai tsauri.

Sama da mutane 600 ne suka halarra, ciki har da mutane kusan 100 da ayyukan ta’addanci ya shafa, daga kasashe 25 na fadin duniya.

An kammala ne da jawabin shugaban taron, kuma mataimakin sakatare janar na MDD kan yaki da ta’addanci, Vladimir Voronkov ya gabatar.

A jawabin, Vladimir Voronkov ya jaddada wasu dabaru 3 da ya kamata a dauka wajen kare hakkokin mutanen da kara ba su tallafin kudi da na shari’a da kiwon lafiya da na lafiyar kwakwalwa da suke bukata.

Jawabin nasa ya kuma duba yiwuwar kaddamar da kungiyar mutanen da ayyukan ta’addanci suka shafa, na ofishin MDD mai yaki da ta’addanci, a shekarar 2023, wadda za ta hada mutanen da kungiyoyinsu da ma kungiyoyin al’umma, domin inganta hakkokinsu.

Taron na wadanda ayyukan ta’addanci ya shafa na duniya, wani gagagrumin ci gaba ne wajen karfafawa duniya gwiwa da bayyana muhimmancin goya musu baya. (Fa’iza Mustapha)