logo

HAUSA

Neman Illata Kasar Sin Ya Haifar Da Matsalar Tattalin Arziki Ga Amurka

2022-09-10 16:40:25 CMG Hausa

Tashar yanar gizo ta Eurasia Review ta kasar Amurka wato nazarin Asiya da Turai, ta ba da rahoton cewa, a kokarinta na neman iko, gwamnatin Joe Biden ta Amurka na neman lahanta ci gaban tattalin arzikin Sin da na yammacin duniya, da kasashen Asiya masu tasowa da ma makomar dukkan kasashe masu tasowa.

Rahoton wanda aka wallafa a ranar 31 ga watan Augusta, ya ruwaito Jack Kemp, mai fashin baki kan harkokin tattalin arziki na kamfanin dillancin labarai na Reuters na cewa, tun farkon 2018, Amurka take aiwatar da matakai da gangan, da zummar illata tattalin arzikin Sin, domin damuwar da take da ita ta karkatar karfin tattalin arziki da rashin daidaito a fannin cinikayya.

Har ila yau, ya ruwaito kwararriya kan harkar tattalin ariziki Anne O. Krueger, na cewa, rikicin cinikayya da gwamnatin Trump ta kaddamar, bai amfani kasar ba, inda ya haifar da illa ga Sin da ita kanta Amurka. Haka kuma mutane da dama sun yi fatan nasarar da Biden ya samu ta zama shugaban kasar, za ta zo da yi wa dangantakar kasashen biyu garambawul, amma akasin haka ne ya faru.

Maimakon haka a cewar rahoton, sai gwamnatin Biden ta dora akan dabarun Trump masu cike da matsaloli, inda ta fara amfani da su a matsayin makami, yayin da suke zaman hadari ga kawayen Amurka. (Fa’iza Mustapha)