logo

HAUSA

Xi Jinping da shugaban AU sun taya juna murna

2022-09-09 11:28:50 CMG Hausa

Yau Jumma’a ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka AU, kana shugaban kasar Senegal Macky Sall, suka aika wa juna sakon murnar cika shekaru 20 da kafa AU da kulla alakar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da AU.

Shugaba Xi ya ce, alakar Sin da AU na dada habaka, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa dankon zumunta tsakanin Sin da Afirka, da kara fadada hadin-gwiwarsu a sabon zamanin da muke ciki. Ya ce yana fatan hada kai tare da Macky Sall da sauran shugabannin kasashe membobin AU, don tabbatar da aiwatar da nasarorin da aka cimma a wajen taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, da ci gaba da marawa juna baya a wasu muhimman batutuwa, da kara wakilcin kasashe masu tasowa a harkokin kasa da kasa, a kokarin bayar da gudummawa ga raya al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya a sabon zamanin da muke ciki.

A nasa bangaren, Macky Sall ya ce, a daidai lokacin da ake cika shekaru 20 da kafa kungiyar AU, shugaba Xi Jinping ya aiko da sakon murna, al’amarin da ya shaida irin dadadden zumuncin dake tsakanin al’ummomin Afirka da Sin. Ya sake jaddada cewa, Afirka na tsayawa haikan kan manufar kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya, da nuna cikakken goyon-baya wajen raya al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)