logo

HAUSA

Wang Yi ya zanta ta wayar tarho da ministan harkokin waje na Iran

2022-09-09 14:32:55 CMG HAUSA

 

A jiya Alhamis ne mamban majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya yi hira da ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian ta wayar tarho kamar yadda aka tsara tun a baya.

Yayin hirar tasu, Wang Yi ya bayyana cewa, ko da yake yanayin duniya na canzawa, duk da haka, bangaren Sin zai bunkasa abokantaka tsakaninsa da Iran, bisa shirye-shiryen shugabannin kasashen biyu, zai kuma karfafa hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ta yadda abokantakar hadin gwiwar Sin da Iran za ta samu sabon ci gaba.

A nasa bangaren, Amir-Abdollahian ya yi fatan taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 zai yi nasara, ya kuma jajantawa bangaren kasar Sin, dangane da girgizar kasar da ta afku a gundumar Luding na lardin Sichuan. Amir-Abdollahian ya ce bangaren Iran zai nuna goyon baya ga shawarwarin bunkasuwar duniya da na tsaron duniya.

Daga nan sai ya gabatar da burin da ake da shi, na kaiwa ga sabon matakin farfado da tattaunawa, game da yarjejeniyar nukiliyar Iran. Yana mai cewa, bangaren Iran ya dade yana himmatu wajen cimma wannan yarjejeniya, amma fa Iran ba za ta amince da bangaren Amurka wanda ya nuna mata karfin tuwo don cimma makasudinsa ba. Har ila yau, Iran na godiya bisa goyon baya da bangaren Sin ke ba shi.

Game da hakan, Wang Yi ya ce, bangaren Sin zai ci gaba da nuna goyon baya ga Iran don kare halastaccen ikonsa. Ya kuma yarda cewa, bangaren Iran yana da basirar tinkarar sauyin da ake ciki, shi ya sa ba kawai yana kiyaye hakkokin kasar na halal, da muradunta ba ne, har ma yana ci gaba da kare martabar cudanyar kasa da kasa. (Safiyah Ma)