logo

HAUSA

Bikin baje koli na CIIE zai samu halartar kamfanoni sama da 280 dake kan gaba a duniya

2022-09-09 10:58:37 CMG HAUSA

Jiya ne, aka gudanar da taron masu saye da sayarwa na reshen bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin masarufi da cinikin ba da hidimma CIIE kana taron shigo da jarin waje na birnin Shanghai, inda aka bayyana cewa, yanzu an kammala aikin yin rajistar kamfanoni da za su halarci bikin, inda fiye da kamfanoni 280 daga cikin 500 dake kan gaba a duniya ne suka tabbatar da aniyarsu ta halartar taron, daga cikinsu kashi 90% sun halarci bikin na bara.

Mataimakin darektan hukumar baje kolin kayayyakin da aka shigo da su kasar Sin Liu Fuxue ya ce, za a gudanar da bikin CIIE karo na 5 a birnin Shanghai kamar yadda aka tsara, daga ran 5 zuwa 10 ga watan Nuwamban wannan shekara.

Bikin na wannan karo zai kai wani sabon matsayi da samun karin abokai da kara nuna kwarewa da sauransu, kuma a karon farko, za a gabatar da karin sabbin kayayyaki. Ya zuwa yanzu, aikin shirye-shiryen bikin na CIIE, ya sauya daga jawo masu baje kolin zuwa jawo jari da kuma shirya nune-nune. (Amina Xu)