logo

HAUSA

Rasha ta haramtawa karin Amurkawa 25 shiga kasar

2022-09-06 10:47:30 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanya karin wasu Amurka 25, cikin jerin mutanen da ta haramtawa shiga kasar, a wani mataki na ramuwar gayya kan matakan muzgunawa Rasha da Amurkan ke dauka.

Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a jiya Litinin, ta ce mutanen da aka haramtawa shiga Rashan sun hada da wasu ’yan majalissar dokokin Amurka, da manyan jami’ai, da ’yan kasuwa, da kwararru a wasu fannoni, da wakilan sashen raya al’adu, ciki har da sakatariyar cinikayya Gina Raimondo.

Sanarwar ta ce, Moscow za ta ci gaba da aiwatar da tsauraran matakai kan Amurka, sakamakon kafar ungulu, da gurgunta alakar kasashen biyu, da ingiza fito na fito da Amurka ke yi.

Ya zuwa yanzu, adadin Amurkawa da Rasha ta kakabawa takunkumai, ciki har da na hana shiga kasar sun kai mutum 1,073, ciki har da shugaban kasar mai ci Joe Biden. (Saminu Alhassan)