logo

HAUSA

Jagorori a Iraqi sun amince su yi aiki tare domin warware takaddamar siyasar kasar

2022-09-06 11:06:25 CMG Hausa

Manyan jagororin siyasa na kasar Iraqi, sun cimma matsaya game da komawa teburin sulhu, domin warware rigingimun dake addabar kasar. An cimma wannan nasara ne yayin zaman da sassan masu ruwa da tsaki a siyasar kasar suka gudanar a jiya Litinin.

Wata sanarwa da ofishin riko na firaministan kasar Mustafa al-Kadhimi ya fitar, ta ce yayin zaman wanda shugaban kasar Iraqi Barham Salih, da kakakin majalissar dokokin kasar Mohammed al-Halbousi, da wakiliyar musamman ta babban magatakardar MDD a kasar Jeanine Hennis-Plasschaert, da sauran jiga-jigan jam’iyyun siyasar kasar suka halarta, an amince a kafa wata tawaga mai wakilcin jam’iyyun siyasa daban daban, wadda za ta tsara dabarun gaggauta gudanar da sahihin zabe, da sake nazarin dokar zabe, da sake inganta hukumar zaben kasar.

Har ila yau, sanarwar ta jaddada bukatar yin gyaran fuska ga tsarin siyasar kasar Iraqi, ta hanyar kafa dokoki masu alaka, da tsare-tsaren ayyukan hukuma, bisa tanadin kundin tsarin mulki a dukkanin matakai da za a aiwatar.

A ’yan makwannin baya bayan nan, Iraqi na fuskantar karuwar rashin jituwa, tsakanin sanannen malamin addinin nan na kasar Muqtada Al-Sadr, da gamayyar jam’iyyun ’yan Shi’a dake majalissar dokokin kasar. (Saminu Alhassan)