logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi nasarar gwajin harba tauraron dan-Adam na Weili mai lamba 1 S3/S4

2022-09-06 15:36:08 CMG Hausa

Yau ne da misalin karfe 10 da mituna 24 na safe, kasar Sin ta yi amfani da rokar Kuaizhou-1A a cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan, inda ta yi nasarar gwajin harba tauraron dan-Adam samfurin Weili Space-1 S3/S4 cikin sararin samaniya kamar yadda aka tsara, kuma aikin harba tauraron dan-Adam din ya samu cikakkiyar nasara.

Wannan shi ne karo na 17 da aka ci nasarar yin amfani da rokar Kuaizhou-1A, wajen aikin harba taurarin dan-Adam zuwa sararin samaniya.  (Ibrahim Yaya)