logo

HAUSA

Kasashen dake da alaka da "Ziri daya da hanya daya" suna fatan karfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannin cinikayyar zamani

2022-09-05 13:29:15 CMG Hausa

Ana gudanar da bikin baje kolin cinikayyar hidima na kasa da kasa na kasar Sin (CIFTIS) na shekarar 2022 a nan birnin Beijing. Wasu daga cikin kasashe, da kamfanoni da ke halartar wannan baje kolin sun fito ne daga kasashen da ke da alaka da shawarar "Ziri daya da hanya daya". Mahalarta taron daga wadannan kasashe sun bayyana cewa, yin amfani da fasahar zamani, ya samar da damammaki wajen bunkasa cinikin hidima a duniya, kuma suna fatan yin hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni da dama a nan gaba.

A cikin yankin nuna hidimomin al'adu da yawon shakatawa na CIFTIS, kasashen da ke da alaka da shawarar "Ziri daya da hanya daya", ciki har da Sri Lanka, sun nuna samfuran al'adun su ga masu sauraro, don kara habaka musayar ciniki ta al'adu. Chiranjaya Udumullage, shugaban kungiyar 'yan kasuwa da masana'antu ta Sin da Sri Lanka, ya bayyana cewa,

 “Yawancin kayayyakin cinikayyarmu suna shiga kasar Sin daidai saboda "Ziri daya da hanya daya". Ina tsammanin wannan kasuwa tana da girma, kuma yanzu akwai dandamali kamar na watsa shirye-shirye kai tsaye ta yanar gizo, wanda zai taimaka wajen bude kasuwa cikin sauki.”

Ya zuwa watan Afrilun bana, kasar Sin ta riga ta sanya hannu kan takardun hadin gwiwa sama da 200, bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya” tare da kasashe 149 da kungiyoyin kasa da kasa 32. Zhu Guangyao, babban sufeto a mataki na biyu na sashen cinikin hidima a ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, ya gabatar da cewa,

 “A shekarar 2021, jimillar kudin kayayyakin ciniki na shige da na fice tsakanin kasar Sin da kasashen dake da alaka da shawarar "Ziri daya da hanya daya", sun zarce dalar Amurka biliyan 110, adadin da ya karu da kashi 33.4 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, hakan ya nuna karfin hadin gwiwar cinikayyar hidima tsakanin kasar Sin da wadannan kasashe, wanda kuma hakan zai kara habaka irin hadin gwiwar su a nan gaba.” (Mai fassara: Bilkisu Xin)