logo

HAUSA

An yi bincike kan kutsen yanar gizo da NSA ta Amurka ta yiwa jami’ar NPU ta Sin

2022-09-05 20:27:40 CMG Hausa

A yau ne, hukumar daidaita mummunar manhajar da ta bata kamfuta ta kasar Sin da kuma kamfanin Qihoo 360 na kasar Sin, suka gabatar da rahotannin binciken batun kutsen yanar gizo da aka yiwa jami’ar koyon ilmin masana’antu ta yankin arewa maso yammacin kasar Sin wato NPU.

Rahotannin sun shaida cewa, ofishin kula da aikin kai harin musamman wato TAO dake karkashin jagorancin hukumar kula da tsaron kasar Amurka wato NSA, ya yi amfani da hanyoyi fiye da 40 wajen yi wa yanar gizon NPU kutse da kuma leken asiri a fannonin tsarin na’urori masu amfani da yanar gizo, da bayanan yanar gizo, da abubuwan dake shafar aikin sarrafa tsarin yanar gizo da sauransu.

Bisa rahotannin binciken da aka gabatar, an ce, hukumar NSA ta shirya sosai na dogon lokaci, don boye ayyukan da ta yi na kutsen yanar gizon NPU da sauran tsarin sadarwa na kasar Sin. Ofishin TAO ya yi amfani da na’urorin kamfuta guda 54 wajen yin kutsen, wadanda suke cikin kasashe 17 kamar Japan, da Koriya ta Kudu, da Sweden, da Poland, da Ukraine da sauransu, kashi 70 cikin dari daga cikinsu kuma, suna makwabtaka da kasar Sin.

Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a gun taron manema labaru da aka yi a yau cewa, mummunan aikin na kasar Amurka ya kawo babbar illa ga tsaron kasar Sin da tsaron bayanan sadarwa na jama’ar kasar, kuma Sin din ta yi tir da hakan, tare da bukatar Amurka da ta yi bayani game da batun da kuma dakatar da irin wannan mugun aiki. (Zainab)